Skip to content
1 Sarakuna 2:5-9

1 Sarakuna 2:5-9

5
“Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.
6
Ka yi da shi gwargwadon hikimarka, amma kada ka bari yă gangara kabari da furfura cikin salama.
7
“Amma ka yi alheri ga ’ya’yan Barzillai mutumin Gileyad, ka sa su kasance a cikin waɗanda suke ci a teburinka. Sun goyi bayana sa’ad da nake gudu daga ɗan’uwanka Absalom.
8
“Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’
9
Amma yanzu, kada ka ɗauke shi marar laifi. Kai mutum ne mai hikima; za ka san abin da za ka yi da shi. Ka kawo furfuransa zuwa kabari da jini.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options