Skip to content
1 Sarakuna 1:43-48

1 Sarakuna 1:43-48

43
Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki.
44
Sarki ya aika shi tare da Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa, suka sa shi a kan dokin sarki,
45
Zadok firist kuwa da annabi Natan sun shafe shi sarki a Gihon. Daga can suka haura suna kirari, birni kuwa ta ɓarke da sowa. Surutun da kake ji ke nan.
46
Ban da haka ma, Solomon ne sarki yanzu.
47
Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa
48
ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’ ”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options