1 Korintiyawa 7:25-35
25
To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji.
26
Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke.
27
In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure.
28
Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.
29
’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su;
30
waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne;
31
masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.
32
Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji.
33
Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa
34
hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta.
35
Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.
Settings