Skip to content
1 Korintiyawa 4:14-17

1 Korintiyawa 4:14-17

14
Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu.
15
Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.
16
Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni.
17
Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options