1 Korintiyawa 4:18-21
18
Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai.
19
Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko.
20
Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko.
21
Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai?
Settings