1 Korintiyawa 4:14-16
14
Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu.
15
Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara.
16
Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni.
Settings