Skip to content
1 Korintiyawa 12:4-11

1 Korintiyawa 12:4-11

4
Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne.
5
Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne.
6
Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.
7
An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa.
8
Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda.
9
Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda.
10
Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna.
11
Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options