1 Korintiyawa 11:4-10
4
Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa.
5
Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan.
6
In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta.
7
Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.
8
Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.
9
Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.
10
Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.
Settings