Skip to content
1 Korintiyawa 1:17-25

1 Korintiyawa 1:17-25

17
Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa.
18
Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.
19
Gama a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”
20
Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba?
21
Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.
22
Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima,
23
amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai,
24
amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah.
25
Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options