1 Tarihi 6:31-47
31
Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
32
Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
33
Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
34
ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa,
35
ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,
36
ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
37
ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
38
ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
39
da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,
40
ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya,
41
ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya
42
ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi,
43
ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi;
44
da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk,
45
ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,
46
ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,
47
ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.
Settings