1 Tarihi 29:24-30
24
Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.
25
Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.
26
Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila.
27
Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima.
28
Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.
29
Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba,
30
tare da yadda mulkinsa da ikonsa da yanayin da suka kewaye shi da Isra’ila da kuma dukan masarautai na dukan sauran ƙasashe.
Settings