2 Tarihi 1:1-6
1
Solomon ɗan Dawuda ya kafa kansa sosai a bisa masarautarsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi ya kuma sa ya zama mai girma sosai.
2
Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai,
3
Solomon tare da dukan taron suka tafi masujadan kan tudu a Gibeyon, gama Tentin Sujadar Allah yana can, wanda Musa bawan Ubangiji ya yi a hamada.
4
Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima.
5
Amma bagaden tagullar da Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, ya yi a Gibeyon a gaba tabanakul na Ubangiji; saboda haka Solomon da taron suka neme nufin Ubangiji a can.
6
Solomon ya haura zuwa bagaden tagulla a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada, ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa dubbai a kansa.
Settings