Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Twins

7 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga ’yan biyu maza a mahaifarta.

  2. Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa.

  3. Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.

  4. Sa’ad da lokaci ya yi da za tă haihu, ashe, tagwaye ’yan maza ne suke cikinta.

  5. Yayinda take haihuwa, ɗaya daga cikinsu ya fid da hannunsa; sai ungonzomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura a hannun, ta ce, “Wannan ne ya fito da farko.”

  6. Amma sa’ad da ya janye hannunsa, sai ɗan’uwansa ya fito, sai ta ce, “Wato, haka ne ka keta ka fito!” Sai aka ba shi suna Ferez.

  7. Sa’an nan ɗan’uwansa wanda yake da jan zare a hannunsa ya fito, aka kuma ba shi suna Zera.