Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Thorn

11 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona.

  2. Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?

  3. Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.

  4. Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.

  5. Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya, haka dariyar wawaye take. Wannan ma ba shi da amfani.

  6. Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya; zan yi mata katanga don kada tă sami hanya.

  7. Mafi kyau a cikinsu yana kama da ƙaya, mafi gaskiyarsu ya fi shingen ƙaya muni. Ranar da Allah zai ziyarce ku ta zo, ranar da masu gadinku za su hura ƙaho. Yanzu ne lokacin ruɗewarku.

  8. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”

  9. Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.

  10. Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya.

  11. Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”