Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ostrich

9 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu,

  2. Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi.

  3. “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.

  4. Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,

  5. ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.

  6. Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba.

  7. Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta.

  8. Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya.

  9. Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.