Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Love of God

7 ayoyi · 35 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,

  2. ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”

  3. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”

  4. Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana,

  5. sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki,

  6. wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu,

  7. wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami.