Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Doctrines of the Gospel: Lead to holiness

6 ayoyi · 23 fannoni

Ayoyi game da Lead to holiness

  1. Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku.

  2. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

  3. Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.

  4. Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

  5. Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne!

  6. Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.