Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Skin

9 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura.

  2. fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau, itacen akashiya,

  3. A bisa waɗannan za su shimfiɗa jan zane, su rufe su da fatun shanun teku, su kuma zura masa sandunansa.

  4. “Za su ɗauki zane mai ruwan shuɗi su rufe wurin ajiye fitilan da yake don fitilu, tare da fitilunsa, lagwaninsa da farantansa, da dukan tulunansa don man amfaninsu.

  5. Sa’an nan su naɗe shi da kuma dukan kayayyakinsa a cikin fatar shanun teku, su sa shi a kan sandan ɗaukarsa.

  6. “A kan bagaden zinariya, za su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi, su kuma rufe shi da fatar shanun teku, sai a zura masa sandunansa.

  7. “Za su ɗauki dukan kayayyakin da ake amfani da su a wuri mai tsarki, su nannaɗe su da zane mai ruwan shuɗi, su rufe shi da fatar shanun teku, sa’an nan a sa su a kan sandan ɗaukarsa.

  8. “Za su kwashe tokar da take a bagaden tagulla, su shimfiɗa zane mai ruwan shuɗi a bisansa.

  9. Sa’an nan su sa a kansa dukan kayayyakin da aka yi amfani da su a bagaden, haɗe da farantai don wuta, cokula masu yatsu don nama, manyan cokula, da darunan yayyafawa. A kansa za su shimfiɗa murfi na fatun shanun teku, su zura sandunan ɗaukarsa.