Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sibmah: A city of Reuben

4 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da A city of Reuben

  1. Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,

  2. Gonakin Heshbon sun bushe, inabin Sibma ma haka. Masu mulkin al’ummai sun tattake inabi mafi kyau, waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer suka bazu ta wajen hamada. Tohonsu sun buɗu suka kai har teku.

  3. Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.

  4. Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka Ya kuringar Sibma. Rassanki sun kai har teku; sun kai har tekun Yazer. Mai hallakarwa ya fāɗo a kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.