Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sherebiah

8 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da ’ya’yansa da kuma ’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne.

  2. Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma ’yan’uwansu guda goma.

  3. Lawiyawa, wato, su Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma’asehiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan da Felahiya, suka koyar da mutane a cikin Dokar yayinda mutane suke a tsaye a can.

  4. A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu.

  5. Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.” “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo.

  6. da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,

  7. Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da ’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya.

  8. Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.