Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shebaniah
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu.
Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.” “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo.
da Hattush, da Shebaniya, da Malluk,
’yan’uwansu kuwa su ne, Shebaniya, da Hodiya, da Kelita, da Felahiya, da Hanan,
da Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,
na iyalin Malluk, Yonatan; na iyalin Shebaniya, Yusuf;