Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Recreation: Jesus takes, from the fatigues of His ministry
Ayoyi game da Jesus takes, from the fatigues of His ministry
To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”
Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.
Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.