Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paralysis: Cured by Jesus
Ayoyi game da Cured by Jesus
Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”
Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”
Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”