Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miscegenation (Intermarriage)

6 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.

  2. Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku.

  3. “Amma in kuka juya baya kuka zama abokai ga waɗanda suka ragu suke zama a cikinku a ƙasashen nan, har kuka yi auratayya da su, kuka haɗa kai da su,

  4. ku tabbata cewa Ubangiji Allahnku ba zai kore muku mutanen ƙasashen nan ba, sai ma su zama muku dutsen tuntuɓe da tarko, za su zama bulala a bayanku, ƙayayyuwa a idanunku, har sai kun hallaka daga wannan ƙasa mai kyau wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.

  5. Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada.

  6. Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera.