Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Melchizedek: King of Salem
Ayoyi game da King of Salem
Sai Melkizedek sarkin Salem ya kawo burodi da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Mafi Ɗaukaka,
ya albarkaci Abram yana cewa, “Allah Mafi Ɗaukaka Mahaliccin sama da ƙasa yă albarkace Abram.
Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome.
Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”