Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Magnificat of Mary

10 ayoyi

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji

  2. ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

  3. gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,

  4. gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne.

  5. Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani.

  6. Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.

  7. Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

  8. Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi.

  9. Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai

  10. ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”