Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Forgetting God: Power to deliver
Ayoyi game da Power to deliver
har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci?
Ba da daɗewa za a ’yantar da ’yan kurkuku; ba za su mutu a kurkuku ba, ba kuwa za su rasa abinci ba.
Gama ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya dama teku domin raƙumansa su yi ruri, Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.