Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Fishermen: Certain apostles

6 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Certain apostles

  1. Da Yesu yana kan tafiya a bakin Tekun Galili, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Siman wanda ake kira Bitrus da ɗan’uwansa Andarawus. Suna jefa abin kamun kifi a tafki, gama su masunta ne.

  2. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”

  3. Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.

  4. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su,

  5. Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare.

  6. Sai Siman Bitrus ya ce musu, “Za ni kamun kifi,” suka ce, “Za mu tafi tare da kai.” Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.