Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da First Fruits: First ripe of fruits, grain, oil, wine, and first of fleece, required as an offering

5 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da First ripe of fruits, grain, oil, wine, and first of fleece, required as an offering

  1. Za ku iya kawo su ga Ubangiji kamar hadaya ta ’ya’yan fari, amma ba za a miƙa su a bagade kamar turare mai ƙanshi ba.

  2. A sa gishiri a dukan hadayunku na hatsi. Kada a rasa sa gishirin alkawari na Allahnku a hadayunku na hatsi, a sa gishiri a dukan hadayunku.

  3. “ ‘In kuka kawo hadaya ta gari na ’ya’yan fari ga Ubangiji, sai ku miƙa ɓarzajjen kawunan sabon hatsin da aka gasa a wuta.

  4. A sa mai da turare a kansa, hadaya ce ta hatsi.

  5. Firist zai ƙone sashe na ɓarzajjen hatsin da kuma mai, tare da turare don tunawa, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.