Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Elimelech
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sunan mutumin, Elimelek ne, sunan matarsa Na’omi; sunayen ’ya’yan nan nasu biyu, su ne Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Betlehem ta Yahuda. Suka kuwa tafi Mowab suka zauna a can.
To, Elimelek mijin Na’omi ya rasu, aka bar ta da ’ya’yanta maza biyu.
To, fa, Na’omi tana da dangi a gefen mijinta da iyalin Elimelek, mutum mai martaba, mai suna Bowaz.
Sai Rut mutuniyar Mowab ta ce wa Na’omi, “Bari in tafi gonaki in yi kala raguwar hatsi a bayan duk wanda na sami tagomashi daga gare shi.” Na’omi ta ce mata, “Ki je, ’yata.”