Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Dothan

7 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai sarki ya ba da umarni ya ce, “Ku je ku tabbatar da inda yake don in aika mutane a kamo shi.” Sai ya sami rahoto cewa, “Yana a Dotan.”

  2. Sai ya aika da dawakai da kekunan yaƙi da babban rukunin soja zuwa can. Suka bi dare, suka kewaye birnin.

  3. Sa’ad da bawan mutumin Allah ya farka ya kuma fita kashegari da sassafe, sai ga mayaƙa tare da dawakai da kekunan yaƙi sun kewaye birni. Sai bawan ya ce, “Ranka yă daɗe! Me za mu yi?”

  4. Sai annabin ya ce, “Kada ka ji tsoro, waɗanda suke tare da mu sun fi waɗanda suke tare da su.”

  5. Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa yă gani!” Sai Ubangiji ya buɗe idanun bawan, ya duba, ya ga tuddai cike da dawakai da keken yaƙin wuta kewaye da Elisha.

  6. Yayinda abokan gāba suka gangaro wajensa, sai Elisha ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ka sa mutanen nan su zama makafi.” Sai Ubangiji ya buge su da makanta kamar yadda Elisha ya roƙa.

  7. Elisha ya ce musu, “Wannan ba ita ce hanyar ba, ba kuma gari ke nan ba, ku bi ni, zan kuwa kai ku wurin mutumin da kuke nema!” Sai ya kai su Samariya.