Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cursing: Shimei curses David

4 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Shimei curses David

  1. Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa.

  2. Ya jajjefi Dawuda da dukan fadawan sarki da duwatsu, ko da yake sojoji da masu gadin sarki na musamman suna kewaye da sarki dama da hagu.

  3. Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai!

  4. Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!”