Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Continents: General references

26 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.

  2. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

  3. Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta.

  4. Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.

  5. Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.

  6. Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.

  7. “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani.

  8. Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?

  9. A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,

  10. yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.

  11. “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.

  12. Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,

  13. sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa.

  14. Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?

  15. “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito,

  16. don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?

  17. Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga.

  18. An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi.

  19. “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?

  20. Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?

  21. Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka.

  22. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.

  23. Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.

  24. Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;

  25. suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.