Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Cherith: A brook near Jericho.
Ayoyi game da A brook near Jericho.
“Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun.
Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”
Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.
Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.
Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba.