Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Botany: Laws of nature in the vegetable kingdom uniform in action

8 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Laws of nature in the vegetable kingdom uniform in action

  1. Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya?

  2. Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.

  3. Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.

  4. “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.

  5. Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya.

  6. Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu.

  7. Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam.

  8. Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta.