Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Architecture

4 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji.

  2. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.

  3. An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja.

  4. Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.