Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ananias: 3. A Christian in Damascus

14 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da 3. A Christian in Damascus

  1. A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”

  2. Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.

  3. Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.”

  4. Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima.

  5. Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”

  6. Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila.

  7. Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”

  8. Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”

  9. Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma,

  10. “Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai.

  11. Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa.

  12. “Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa.

  13. Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji.

  14. Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’