Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ajah

7 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.

  2. To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”

  3. Amma sarki ya ɗauki Armoni da Mefiboshet, ’ya’ya biyu maza waɗanda Rizfa ’yar Aiya ta haifa wa Shawulu, tare da ’ya’ya maza biyar na Merab ’yar Shawulu, waɗanda ta haifa wa Adriyel ɗan Barzillai, mutumin Mehola.

  4. Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir.

  5. Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba.

  6. Da aka gaya wa Dawuda abin da Rizfa ’yar Aiya ƙwarƙwaran Shawulu ta yi,

  7. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana.