Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflicted

31 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi,

  2. to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.

  3. aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

  4. Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.

  5. Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji.

  6. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.