Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Accursed
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
kada ku bar jikinsa a kan itacen yă kwana. Ku tabbata kun binne shi a ranar, domin duk wanda aka rataye a kan itace la’ananne ne ga Allah. Kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo.
Birnin da dukan abin da yake cikinta za a miƙa su ga Ubangiji. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye ’yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.
Amma Isra’ilawa ba su yi aminci game da kayan da aka hallaka ba; Akan ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera, na kabilan Yahuda ya kwashi waɗansu abubuwa, saboda haka fushin Ubangiji ya sauka a kan Isra’ilawa.
’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta.
“A cikinta ba za a ƙara jin jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba, ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba; duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari za a ce ya mutu a kurciya ne kawai; duk wanda bai kai ɗari ba za a ɗauka la’antacce ne.
Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada!