Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abiram: 1. An Israelite who conspired with Dathan against Moses and Aaron

4 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da 1. An Israelite who conspired with Dathan against Moses and Aaron

  1. ’ya’yan Eliyab maza kuwa su ne, Nemuwel, Datan da Abiram. Datan da Abiram nan, su ne shugabannin mutanen da suka tayar wa Musa da Haruna, suna kuma cikin waɗanda suka bi Kora sa’ad da ya tayar wa Ubangiji.

  2. Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora, wanda ƙungiyarsa ta mutu sa’ad da wuta ta cinye mutum 250. Wannan kuwa ya zama alamar faɗakarwa.

  3. ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.

  4. Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram.