Skip to content

Cushi

5 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Cushi

  1. Sai Yowab ya ce wa wani mutumin Kush, “Je ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Mutumin Kush ɗin kuwa ya rusuna wa Yowab, sai ya ruga a guje.

  2. Ahimawaz ɗan Zadok ya sāke ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru, ina roƙonka bari in bi bayan mutumin Kush nan.” Amma Yowab ya ce, “Ɗana me ya sa kake so ka je? Ba ka da labarin da zai jawo maka lada.”

  3. Ya ce, “Ko mene ne zai faru, ina so in ruga da gudu.” Sai Yowab ya ce, “Ruga!” Sai Ahimawaz ya sheƙa a guje ya bi ta hanyar fili ya riga mutumin Kush nan.

  4. Sai ga mutumin Kush ya iso ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, ka ji labari mai kyau! Ubangiji ya cece ka yau daga dukan waɗanda suka tayar maka.”

  5. Sarki ya ce wa mutumin Kush, “Saurayin nan Absalom, yana nan lafiya?” Mutumin Kush ya ce, “Allah yă sa abokan gāban ranka yă daɗe, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”