Zabura8
Listen to this chapter
0:00
0:00
1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.
2
Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
3
Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,
4
wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?
5
Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
6
Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
7
dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,
8
tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
9
Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
Use ← → arrow keys to navigate
Settings
Reading Style
Typeface
Font Size px
Options
Study Note