Skip to content

Zabura76

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.
2
Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.
3
A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela
4
Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.
5
Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.
6
A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.
7
Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?
8
Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,
9
sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela
10
Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.
11
Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.
12
Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options