Skip to content

Zabura57

1
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.
2
Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.
3
Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.
4
Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.
5
Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
6
Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela
7
Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
8
Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka.
9
Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane.
10
Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari.
11
Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options