Tsallake zuwa abun ciki

Zabura2

Tawayen al’ummai

1
Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?
2
Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.
3
Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”

Ubangiji yana dariya da makircinsu

4
Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.
5
Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,
6
“Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”

Umurnin Allah da ikon Ɗan

7
Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka.
8
Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.
9
Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”

Gargaɗin ƙarshe da kira zuwa ga miƙa wuya

10
Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.
11
Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
12
Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options