Tsallake zuwa abun ciki

Zabura126

Tunawa da Maidowa Cikin Farin Ciki

1
Waƙar haurawa. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.
2
Bakunanmu sun cika da dariya, harsunanmu da waƙoƙin farin ciki. Sai ana faɗi a cikin al’ummai, “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
3
Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu, mun kuwa cika da farin ciki.

Addu’ar Cikakkiyar Maidowa da Girbi

4
Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji kamar rafuffuka a Negeb.
5
Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
6
Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options