Tsallake zuwa abun ciki

Zabura123

Daga Sama Ana Kallon Ubangiji

1
Waƙar haurawa. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.
2
Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.

Addu’ar Jinƙai Cikin Raini

3
Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa.
4
Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options