Tsallake zuwa abun ciki

Zabura121

Mahajjaci Ya Daga Idonsa Sama

1
Waƙar haurawa. Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?
2
Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.

Mai Tsaro da Ba Ya Barci

3
Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
4
tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.
5
Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6
rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.

Kiyaye Madawwami Mai Cikakken

7
Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;
8
Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.
Use arrow keys to navigate
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options