Skip to content

Zabura 114

Allah Ya Fitar da Isra’ila daga Masar 1–2

1
Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,
2
Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa.

Halitta Ta Amsa Ga Kasancewar Allah 3–4

3
Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya;
4
duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.

Tambayar Halitta 5–6

5
Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya,
6
ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?

Kasancewar Ubangiji Na Bukatar Tsoro 7–8

7
Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub,
8
wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.